Skip to main content
Question
Pi Network
Asked a question 2 months ago

Shin wai menene Pi network?

Where am I?

In Amsa you can ask and answer questions and share your experience with others!

Pi network

Pi network wani nau'in kuɗi ne (cryptocurrency) wanda ake iya amfani dashi ba tare da an rike shi a hannu ba.

Wato ma'ana shi Pi kuɗi ne kamar su Bitcoin, Ethereum da dai sauransu.

Su waɗannan kuɗi ana iya mining ɗin su, wato ana iya samun su ta hanyar amfani da wayar hannu kamar su Android, Iphone ko kuma da hanyar amfani da Computer.

Shin wai Pi network gaskiya ne?

Tambaya me kyau, idan wannan itace tambayar ku to amsar itace Ehh.

Pi network gaskiya ne, kuma babu damfara a cikin sa.

Hasali ma ai ba investing ɗin kudin ku kuka yi ba, babu yadda za'ayi a damfare ku.

Shin Pi network yana da daraja?

Ba kamar yadda kuke zato ba, Pi network bashi da daraja kamar irin ta Bitcoin ko Ethereum.

Bitcoin guda ɗaya (1) a yanzu haka yana kaiwa 8,691,447.70, wato naira miliyan takwas da dubu ɗari shida da wani ɗoriya.

Wanda idan ka kwatanta shi da Pi zaka ga Pi guda dubu ɗaya (1000) a yanzu haka farashin sa bai wuce 2,202.83, wato naira dubu biyu da ɗari biyu da ɗoriya ba.

Shin yaushe darajar Pi zata daukaka?

Ana sa ran zuwa nan da 2025 darajar Pi zata ɗaukaka, wanda hasashen masana ya bayyana cewa Pi guda ɗaya zai iya kaiwa 700.

Bambanci tsakanin Pi da saura

Bambance-bambance tsakanin Pi da kuma abokan hamayyar sa wato irin su Bitcoin da Ethereum na da dama.

Kaɗan daga cikin misalan sune:

Amfani da wayar hannu

Duba da cewar duk sauran abokan hamayyar Pi kamar su Bitcoin da Ethereum suna bukatar Computer idan zakayi mining, shi Pi yasha bam-bam, zaka iya mining Pi a saukake ta hanyar amfani da wayar hannu.

Related Questions

No related questions.